Wannan shi ne karon farko da sabuwar hukumar kolin kasar Sin ta kira taro, tun bayan kammala babban taro karo na 19 na wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a bara. A yayin taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnati, inda ya takaita ayyukan da gwamnatin kasar Sin ta gudanar a cikin shekaru biyar da suka shige, da kuma bayar da shawarwari game da ayyukan da gwamnati za ta yi a bana. Li ya ce, ya kamata gwamnati ta gudanar da ayyukanta daidai bisa tunanin Xi Jinping ta fuskar tattalin arziki irin na tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin a cikin sabon zamani, da kuma warware matsalar rashin samun daidaito yayin da ake neman bunkasuwa, da kuma kara kokarin yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje. Firaministan ya kuma jaddada cewa, ya zama dole a warware matsalolin da jama'ar kasa suka fi mai da hankali a kai, ta yadda rayuwarsu za ta kara inganta.
Har wa yau, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar NPC karo na 12, kana babban sakataren kwamitin, Wang Chen, ya yi bayani kan daftarin shirin yiwa kundin tsarin mulkin kasa gyaran fuska. (Murtala Zhang)