in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labarun Rasha sun yaba wa sakamakon da aka samu a yayin taron shugabannin kasashen BRICS
2017-09-06 11:02:01 cri
A jiya Talata ne aka kammala taron shugabannin kasashen BRICS a birnin Xiamen cikin nasara. A 'yan kwanakin baya, kafofin watsa labaru na kasar Rasha sun mai da hankulansu wajen watsa labaru masu tarin yawa game da taron, da kuma sakamakon da aka fatan samu a yayin taron.

Jaridar "Independence" ta Rasha ta wallafa wani rahoto da ke cewa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya shugabanci taron tattaunawa a tsakanin kasashe da tattalin arzikinsu ke samu saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa, ya kuma bayar da wani muhimmin jawabi, inda ya bayyana ma'anar sabon tsarin BRICS+, da kuma nauyin dake kan tsarin. Wannan rahoto dai ya ce, tsarin BRICS+ wani tunani ne mai ma'ana dake da kyakkyawar makoma. Kuma yanzu haka dangantakar dake tsakanin kasa da kasa na samun sauye-sauye sosai, wannan tsarin BRICS+ zai samar da dama ga kungiyoyin tattalin arziki daban daban, wajen samun sabon mukaminsu a duniya domin cin moriya tare.

Sannan wakilin bankin ajiya na Rasha dake nan kasar Sin, ya nuna cewa, bangaren Sin ya ba da shawarar bunkasa tsarin BRICS+, ba ma kawai domin fatan ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa gaba ba, har ma yana kokarin kara yin muhawara tsakanin kasashe masu sukuni da masu tasowa, wato yana son kafa wata sabuwar dangantaka tsakanin kasashe masu arziki da kasashe masu tasowa.

Bisa rahotannin da kafofin watsa labaru na Rasha suna wallafa, an ce, a yayin taron manema labaru da ya gudana bayan taron BRICS, shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana cewa, shugabannin kasashen BRICS sun samu nasarar yin shawarwari tsakaninsu, kuma kasar Sin, wato mai masaukin bakin taron, ta sauke dukkan nauyin dake bisa wuyanta, har ma ta sa sabon kuzari ga kokarin kara bunkasa tsarin BRICS.

Shugaba Putin ya jaddada cewa, ko shakka babu, tsarin BRICS yana da wata makoma mai haske, yana kuma iya wakiltar moriyar kasashe da tattalin arzikinsu ke samu saurin bunkasuwa, da kasashe masu tasowa gaba daya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China