Yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da manema labarai na gida da na kasashen waje a cibiyar taron kasa da kasa ta birnin Xiamen, inda ya yi bayani kan taron shugabannin kasashen BRICS karo na 9 da taron tattaunawa tsakanin kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki da kasashe masu tasowa.
Xi ya nuna cewa, jiya Litinin aka rufe taron shugabannin kasashen BRICS cikin nasara, aka kuma zartas da "sanarwar shugabannin kasashen BRICS ta Xiamen", inda aka sake jaddada tsarin BRICS na gudanar da hadin gwiwa mai moriyar juna ba tare da rufa rufa ba, da sakamakon da aka samu a cikin shekaru goma da suka gabata, tare kuma da tsara wani sabon shiri game da karfafa huldar abokanaka dake tsakanin kasashen BRICS. Shugabannin kasashen sun bayyana aniyyar cewa, za su hada kai matuka tare domin kara zurfafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a cikin shekaru goma masu zuwa.(Jamila)