A cewar Mista Geng, yayin da suke hadin gwiwa da juna, kasashen BRICS suna girmama juna, da kokarin neman ra'ayi daya. Suna kuma tattaunawa da juna a ko yaushe, don haka a cikinsu babu shugaba. Suna hadin gwiwa ne don kare muradun juna, sa'an nan suna nuna ra'ayi bai daya na kasashe masu tasowa.
Ya ce, babbar manufar hadin gwiwar BRICS ita ce "musayar ra'ayi ba tare da kiyayya da wani ba, da zama tare da juna amma babu kulla kawance". Don haka ana martaba kundin tsarin MDD, da manyan ka'idojin kasa da kasa, don neman samar da wata kungiya ta bai daya da ta shafi muradun 'yan Adam baki daya.(Bello Wang)