A ranar 6 ga wata, shugaba Conde ya halarci taron baje koli na kasashen Sin da Larabawa da aka yi a birnin Yinchuan na kasar Sin, inda ya bayyana cewa, taron kolin kasashen BRICS ya samar wa kasashen Afirka damammaki masu kyau wajen neman ci gaba.
Ya ce, kasar Sin wadda tattalin arzikinta ke saurin bunkasa tana iya kasance abin koyi ga kasashen Afirka, ta yadda kasashen Afirka za su iya koyon darussa da fasahohin kasar Sin domin raya kansu.
A yayin ziyararsa a kasar Sin, shugaba Conde ya kuma kulla wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa da kasar Sin a madadin kungiyar AU da kasar Guinea. (Maryam)