in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya yi kira da a aiwatar da yarjejeniyar Syria da aka cimma
2018-02-26 19:51:10 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bukaci dukkan bangarorin da rikicin Syria ya shafa da su martaba kudurin MDD mai lamba 2401 da aka cimma game da tsagaita bude wuta na kwanaki 30 a kasar da yaki da wargaza.

Guterresd ya ce kudurin kwamitin sulhun zai yi tasiri ne kadai, idan har aka aiwatar da shi yadda ya kamata. Kamar yadda ya bayyana yayin da yake jawabi a zaman bude taron hukumar kare hakkin bil-Adan ta MDD karo na 37.

A ranar Asabar ne dai kwamitin sulhun MDD ya amince da kudurin ba tare da wata hamayya ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China