in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya maraba da zartas da kudurin tsagaita bude wuta da kwamitin sulhu ya yi
2018-02-25 12:52:46 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Ma Zhaoxu ya ce, ya yi maraba da zartas da kuduri game da tsagaita bude wuta a duk fadin kasar Syria, yana ma fatan za a tabbatar da kudurin a duk fannoni.

Ma ya bayyana haka ne bayan kwamitin sulhu ya zartas da wannan kuduri mai lamba 2401, a cewarsa, an cimma wannan kuduri ne bayan mambobin kwamitin sulhu suka yi shawarwari da neman ra'ayin bai daya. A cikin kudurin din an girmama mulkin kai, da 'yancin kai da kuma cikakken yanki na kasar Syria, an kuma bukaci bangarori daban daban su dakatar da ayyukan gaba da juna, da sassauta halin jin kai da ake ciki a kasar, kana da nuna goyon bayan kasar wajen fitar da nakiyoyin da aka binne a kasa, da kuma ci gaba da yaki da ta'addanci da dai sauransu.

Ma ya kara da cewa, kasar Sin ta sa himma wajen shiga shawarwarin, ta kuma yin kokari sosai da nufin cimma ra'ayin bai daya tsakanin mambobin kwamitin sulhu.

A jiya ranar Asabar, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2401 baki daya, inda aka bukaci a tsagaita bude wuta a kalla 30 a duk fadin kasar Syria. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China