Bugu da kari, an lura cewa, a watan Janairu na shekarar bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da muhimmin jawabi mai take "tabbatar da makomar bil Adama cikin hadin gwiwa" a hedkwatar MDD dake birnin Geneva, inda ya yi bayani kan muhimmiyar ma'ana wajen karfafa dunkulewar mutanen kasa da kasa, lamarin da ya janyo hankula da kuma samu yabo daga kasashen duniya kwarai da gaske.
Sa'an nan, a ranar 1 ga watan Maris, a madadin kasashe 140, kasar Sin ta fidda sanarwar hadin gwiwa mai taken "ingantawa da kiyaye hakkin bil Adama, da kuma tabbatar da makomar bai daya ta dan Adam cikin hadin gwiwa" a yayin taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD karo na 34, inda ta sanar da cewa, tabbatar da makomar bil Adama cikin hadin gwiwa tana da muhimmiyar ma'ana wajen raya ayyukan kare hakkin dan Adam a nan duniya, sanarwar ta kuma sami amincewa daga kasashen duniya.
Bugu da kari, sanarwar ta ce, ma'anar tabbatar da makoman bil Adama cikin hadin gwiwa ita ce tabbatar da zaman daidai wa daida na kasa da kasa, yin shawarwari da hadin gwiwa da kuma neman dauwamammen ci gaba, wadda ta samu yabo da goyon baya na kasa da kasa. (Maryam)