in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani rahoton UNICEF ya ce 8 cikin wurare 10 mafi hadari ga jarirai sun kasance a yankin kudu da hamadar Sahara
2018-02-21 12:25:10 cri

Asusun kula da kananan yara na MDD wato UNICEF, ya ce 8 cikin wurare 10 mafi hadari ga jarirai su kasance a yankin kudu da hamadar Sahara.

Cikin rahoton da ya fitar jiya Talata game da mace-macen jarirai, asusun ya ce mutuwar jarirai a duniya musammam a kasashe mafi talauci na ci gaba da karuwa.

Rahoton ya bayyana Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a matsayin kasa mafi hadari ta biyu a duniya bayan Pakistan, kana kasa mafi hadari ga jarirai a nahiyar Afrika.

Rahoton ya ce kasashen Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Somaliya da Lesotho da Guinea Bissau da Afrika ta kudu da Cote d'Ivoire da Mali da Chadi, su ne wurare 8 mafi hadari a nahiyar Afrika, inda mata masu juna biyu ke samun rashin kulawa yayin haihuwa saboda talauci da rikice-rikice da kuma rashin ingantattun asibitoci.

Har ila yau, rahoton ya bayyana mutuwar jarirai 27 cikin haihuwa 1,000 a matsayin matsakaicin mataki na mace-mace jarirai a kasashe marasa karfin tattalin arziki.

A kasashe masu karfin tattalin arziki kuwa, jarirai 3 ne cikin haihuwa 1,000 ke mutuwa. Yana mai cewa jarirai da ake haihuwa a yankuna masu hadari sun fi fuskanatar hadarin mutuwa sau 50 a kan wadanda ke kasashe masu karfi.

Bugu da kari, rahoton ya ce sama da kaso 80 na jarirai na mutuwa ne saboda ba su isa haihuwa ba ko kuma matsaloli da ake samu yayin haihuwarsu ko kuma kwayoyin cuta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China