in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fasahar hada-hadar kudade ta yanar gizo a Afirka za ta bukasa nan da shekarar 2020
2018-02-16 12:34:36 cri

Mataimakiyar shugaban rukunin bankin Eco na nahiyar Afirka, Luck Mbabazi ta bayyana cewa, nan da shekarar 2020, yawan kudaden hada-hada ta yanar gizo a nahiyar Afirka zai karu daga kimanin dala miliyan 200 zuwa dala biliyan 3.

Alkaluman na nuna cewa, yadda ake hada-hadar kudade ta hanyar fasahar zamani a Rwanda ya karu da kaso 11 cikin 100 a rubu'in farko na shekarar 2017 da ta gabata, wato daga dala miliyan 1.37 a shekarar da ta gabata zuwa dala miliyan 1.57.

Jami'ar ta bayyana hakan ne yayin rufe taron kolin fasahar kere-kere ta duniya da aka kammala a birnin Kigalin kasar Rwanda.

Ta ce, fasahar hada-hadar kudade ta zamani tana samarwa sabbin kasuwannni damammakin masu tarin yawa, da zabi masu yawa da hanzarta isar da kayayyaki.

Wasu alkaluman kididdiga da rukunin bankin na ECO ya fitar sun nuna cewa, nahiyar Agorka ce ke kan gaba a fannin hada-hadar kudade ta yanar gizo, adadin da ya kai kaso 57.6 cikin 100 na yawan mutane 174 a duniya da suka bude asusun ajiya ta wayar salula.

Taron wanda aka kammala a jiya Alhamis, ya zakulo sabbin hanyoyin amfani da fasahar hada-hadar kudade ta yanar gizo, inda kimanin shugabanni a wannan fanni daga kasashen Afirka da sauran kasashen duniya 250 suka halarta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China