in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taro shiyya na FAO karo na 30 a kasar Sudan
2018-02-20 11:56:29 cri

A jiya Litinin ne, aka bude taron shiyya na hukumar samar da abinci da aikin gona ta MDD(FAO) karo na 30 a Khartoum, babban birnin kasar Sudan.

A jawabinsa yayin bude taron, mataimakin babban darektan hukumar FAO kana wakilin hukumar mai kula da nahiyar Afirka Bukar Tijani, ya bayyana kudurin hukumarsa na taimakawa kasashen nahiyar Afirka wajen magance kalubalen talauci da yunwa da suke fuskanta.

Shi ma a nasa jawabin, ministan albarkarun dabbobi na kasar Sudan Bushara Juma Aro, ya ce, manufar taron ita ce samar da abinci da kuma tsaronsa ga kowa. Sai dai kuma ya ce, muddin ana fatan cimma wannan buri, wajibi ne a zakulo hanyoyi da matakan da suka dace kan yadda za a zage damtse, a bangaren aikin gona ko kiwon dabbobi.

Taken taron na kwanaki biyar, shi ne samar da ci gaba mai dorewa a fannin aikin gona da tsare-tsaren samar da abinci a nahiyar Afirka: matakan samar da guraben ayyukan yi ga matasan nahiyar.

Jami'ai daga kasashe kimanin 50 da ministocin aikin gona 38 daga kasashen Afirka ne ke halartar taron, baya ga mahalarta 450, wadanda suka hada da manyan masana da kwararru daga Afirka da kuma wasu kasashe biyar dake halartar taron a matsayin 'yan kallo, da kuma kungiyoyin kasa da kasa 17. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China