A ranar Jumma'a shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga Cyril Ramaphosa bayan zabensa a matsayin sabon shugaban kasar Afrika ta kudu.
A sakonsa na taya murnar, Xi ya ce, Ramaphosa ya kasance wani dadadden amini ga al'ummar sinawa, wanda ya bada gagarumar gudunmowa wajen bunkasa cigaban dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Xi ya ce, yana matukar bada muhimmanci game da cigaban dangantaka tsakanin Sin da Afrika ta kudu, ya kara da cewa, a shirye yake ya yi aiki tare da Ramaphosa don daga matsayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani babban mataki.
Shugaban na Sin ya ce, bangarorin biyu suna tallafawa juna wajen shirya taron kolin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika wato FOCAC wanda ake shirin gudanarwa a wannan shekarar a Beijing tun bayan wanda aka gudanar a Johannesburg, kana da hadin gwiwar kungiyar kasashen BRICS, wanda ya kunshi kasashen Sin, Afrika ta kudu, Brazil, Rasha da India. (Ahmad Fagam)