in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan kafofin watsa labaran Nijeriya sun nuna yabowa kan tsarin siyasa da manufar neman bunkasuwar tattalin arzikin Sin
2018-02-08 11:01:08 cri
Kwanan baya, manyan kafofin watsa labarai na kasar Nijeriya sun fidda wasu bayanai, inda suka nuna yabowa kan tsarin siyasar gurguzu na kasar Sin, da kuma manufofin kasar wajen neman bunkasuwar tattalin arziki bisa moriyar al'ummar kasa.

A ranar 4 ga wata, jaridar Leadership ta wallafa sharhin da yar jarida Bukola Ogunsina ta rubuta, inda ta yi bayani kan tsarin siyasar gurguzu na kasar Sin, kuma ta ba da shawara ga kasashen Afirka da su zabi tsarin siyasar su bisa halayen da suke ciki, wanda zai dace da bunkasuwar kasashen Afirka.

Haka kuma, ta ce, a yayin cikakken zaman taron wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin wato JKS karo na 19, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, tsarin gurguzu na kasar Sin ya shiga sabon zamani, lamarin da ya janyo hankulan al'ummomin kasa da kasa kan tsarin siyasar kasar Sin.

Haka kuma, tsarin siyasa na kasar Sin shi ne tsarin gurguzu na musamman dake dacewa da halin da kasar Sin take ciki, kuma ya kamata a yi nazari kan tsarin siyasar kasar Sin da kuma JKS, ta haka ne za a gane babban sakamakon da kasar Sin ta samu ta fuskar samun bunkasuwa.

Bugu da kari, ta ce, ya kamata kasashen Afirka su zabi tsarin siyasar su bisa halayen da suke ciki, domin hakan zai dace da bukatun al'ummomin kasar wajen neman ci gaba bisa fannoni daban daban.

A ranar 5 ga wata kuma, jaridar Herald, da jaridar Citizen, da jaridar The Sun da jaridar The Guardian da dai sauran su, wato manyan kafofin watsa labarai na kasar ta Nijeriya, sun gabatar da jawabin da tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi ya yi a jami'ar Yale ta kasar Amurka, inda ya nuna yabo matuka kan nasarorin da kasar Sin ta samu, wajen raya tattalin arziki da zaman takewar al'umma. Mr. Obi na ganin cewa, idan aka kwatanta da babbar nasarar da kasar Sin ta cimma a yayin da ake aiwatar da muradun ci gaban karni na MDD, za a gane cewa, kasashen Afirka ba su zabi hanyar da ta dacewa bunkasuwarsu ba, don haka ya kamata su yi koyi daga kasar Sin, musamman ma a fannin neman bunkasuwar kasa bisa moriyar al'ummomin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China