in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Mutane fiye da miliyan 385 za su je yawon shakatawa a lokacin bikin bazara
2018-02-06 20:40:08 cri
Sinawa kimanin miliyan 385 ake sa ran za su je yawon shakatawa a cikin kasar, yayin bikin bazara, bikin gargajiya mafi muhimmanci ga al'ummar Sinawa, wanda zai fara daga tsakiyar watan da muke ciki,

Wang Xiaofeng, mataimakin shugaban hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin, shi ne ya yi hasashen hakan a yau Talata a birnin Beijing fadar mulkin kasar. A cewarsa, wannan adadi ya karu da kashi 12 bisa 100 idan aka kwatanta kan bara. Ya ce, yadda ake bulaguro a wannan lokaci zai sa masu sana'ar yawon shakatawa samun kudaden da za su kai Yuan biliyan 476, wanda ya karu da kashi 12.5 cikin 100 a kan na bara.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China