in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: za a ci gaba da kokarin dakile fasa-kwaurin shara
2018-02-06 20:12:56 cri
Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya furta a yau Talata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, cewa kasar za ta ci gaba da kokarin neman biyan bukatunta na gina wata kasa mai kyakkyawan muhalli, inda za ta dauki jerin matakai don dakile yadda ake fasa kwaurin shigo da shara cikin kasar Sin.

Kafin haka, babban darektan hukumar kare muhalli ta MDD, Erik Solheim, ya furta cewa, yadda kasar Sin take kokarin hana shigo da shara cikin kasar, wani sako ne ga wasu kasashe masu sukuni, wanda ya bayyana cewa kamata ya yi a inganta tsarin bola-jari, da rage samar da kayayyakin da al'umma ba ta bukatarsu.

A nasa bangaren, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce gwamnatin kasar Sin ta dauki matakin hana shigo da shara cikin kasar sabo da muhimmiyar manufarta ta kare muhalli, da tabbatar da lafiyar al'ummar kasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China