in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoton bincike kan yanayin makaman nukiliya da Amurka ta gabatar bai dace da halin da ake ciki yanzu ba
2018-02-05 20:09:50 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau Litinin a nan birnin Beijing cewa, rahoton bincike kan yanayin makaman nukiliya da kasar Amurka ta gabatar, ya sabawa yanayin shimfida zaman lafiya da samun ci gaba a duniya.

Geng Shuang ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, rahoton ya yi kama da rahoton manufofin tsaro da rahoton dabarun tsaron kasa da kasar Amurka ta gabatar a kwanakin baya, wanda yake da ra'ayin yakin cacar baka dake tsakanin kasashe masu tsarin jari-hujja da masu bin tsarin gurguzu, da ra'ayin yin takara a tsakanin kasa da kasa wadanda yawan ribar da suka samu ta yi daidai da yawan hasarar da sauran kasashe suka tabka, da bayyana ra'ayin siyasa bisa yanayin wuri da yin takara a tsakanin manyan kasashe, da nanata rawar da makaman nukiliya ta taka yayin da ake aiwatar da manufofin tsaron kasa, da yin watsi da kiraye-kirayen da kasashen duniya suke yi game da rage makaman nukiliya. Ya ce wannan rahoto ya sabawa kokarin da ake na shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya.

Hakazalika, Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin ba za ta shiga gasar makaman nukiliya ta ko wace irin fuska ba, da ci gaba da kiyaye yawan makaman nukiliya don bukatar tsaron kasar. Manufar kasar Sin kan wannan batu ba zai canja ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China