in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi Allah wadai da kisan wani Basine da aka yi a Pakistan
2018-02-06 20:10:42 cri
A kwanakin baya ne aka harbi wani Basine a kasar Pakistan, dangane da batun, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya furta a yau Talata cewa, kasar Sin ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa dan kasarta, za ta kuma mai da hankali kan yadda ake kula da batun, gami da samar da taimako ga iyalan mamacin ta yadda za su je su karbi gawarsa.

Geng ya yi furucin ne yayin wani taron manema labaru da aka kira a birnin Beijing fadar mulkin kasar ta Sin, inda ya ce, kasar Sin tana goyon bayan matakan da gwamnati da sojojin kasar Pakistan suke dauka na yaki da ta'addanci da tabbatar da kwanciyar hankali. Ban da haka, kasar Sin na da imanin cewa gwamnatin Pakistan za ta dauki matakan da suka wajaba don tabbatar da tsaron Sinawa dake kasar Pakistan.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China