Haka kuma, shugaban ofishin kwamitin sa ido kan aikin ba da ilmi na gwamnatin kasar Sin, kana shugaban hukumar sa ido kan aikin ba da ilmi ta ma'aikatar ilmi ta kasar Sin He Xiuchao ya yi bayani cewa, tun lokacin da aka bullo da tsarin a shekarar 2013, ya zuwa yanzu, kimanin masu sa ido kan aikin ba da ilmi dubu 120 ne suke gudanar da aikin a makarantun dake sassa daban daban na kasar Sin, a kokarin da ake yi na ci gaba da kyautata tsarin gudanar da ayyuka, da kafa hukumomin da abin ya shafa da kuma kara kwarewa da karfin iko ga masu aikin sa ido da dai sauransu.
Rahotanni na cewa, muhimman ayyukan da masu aikin sa ido kan aikin ba da ilmi za su gudanar, sun hada da kula da yadda ake gudanar da harkokin makarantu, kula da yanayi da malamai da dalibai ke ciki a fannin ba da ilimi, da kuma samar da tsaro a makarantu da dai sauransu. Kuma aikin yana da muhimmanci matuka wajen inganta ayyukan ba da ilmi. (Maryam)