Sin za ta yi bukukuwan murnar bikin bazara cikin birane sama da 400 na kasa da kasa
Yau Talata, mataimakin ministan harkokin al'adu na kasar Sin Yang Zhijin ya bayyana a birnin Beijing cewa, a yayin bikin bazara na shekarar bana, kasar Sin za ta yi bukukuwan murnar bikin a birane sama da dari 4 na kasa da kasa, domin mika sakon murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajia ta kasar Sin.
Bisa labarin da aka samu, an ce, an tsara shirye-shirye da dama da suka hada da wasan kwaikwayo, da bikin baje-koli cikin wuraren ibada, da liyafar dandana abincin Sin da dai sauransu, wadanda za a yi a kasashe da kuma yankuna sama da 130, ciki har da kasashe da yankuna guda 53, da shawarar "Ziri daya da hanya daya" take shafarwa. (Maryam)