Ta hanyar wannan manhaja, matafiya suna iya zabar hanyar da za su bi bisa irin bayanai da aka samar musu don tabbatar da cewa, sun isa garuruwansu ba tare da wata matsala ba.
Bugu da kari, matafiya za su iya amfani da manhajar ta Amap wajen neman adireshin tashoshin bayar da hidima sama da 80, domin a duba lafiyar ababen hawansu ko sayan abinci.
A ranar 16 ga watan Fabrairu ne dai za a yi bikin Bazana na wannan shekara, inda ake sa ran za a kwashe kwanaki 40 ana yin tafiye-tafiyen bikin wanda aka fara tun daga jiya Alhamis.
Ana kuma sa ran jama'a za su yi zirga-zirga kusan biliyan 2 da miliyan 48 ta hanyoyin mota a lokacin bikin na wannan shekara.
Bikin Bazara dai, shi ne biki mafi muhimmanci ga al'ummar Sinawa. Inda daruruwan miliyoyin Sinawa ke komawa garuruwansu don ganawa da iyalai, 'yan uwa da abokan arziki. A lokacin ne kuma bangaren sufurin kasar ke kara bullo da matakai don ganin komai ya tafi lami lafiya.(Ibrahim)