in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da shagulgulan bikin Bazara a sassan duniya da dama
2017-01-31 12:49:31 cri
Rahotanni daga sassan duniya da dama, na nuna cewa an gudanar da bikin Bazara na al'ummar Sinawa a wurare masu yawa.

A biranen Landan da New York na Amurka, an gudanar da wasan tartsatsin wuta, da kunna fitilo na musamman domin shagulgulan kewayowar shekarar zakara, bisa kalandar gargajiya ta Sinawa.

A kasar Canada kuwa, firaministan kasar Justin Trudeau, ya jagoranci wata tawagar shugabannin kasar zuwa yankin da Sinawa ke zaune ko "Chinatown" wanda ke Vancouver, inda aka yi kade kade da raye raye, a wani bangare na shagulgulan shigowar sabuwar shekarar ta Sinawa.

Bikin Bazara dai shi ne bikin gargajiya mafi girma ga Sinawa, ana shagulguwa tare da haduwa da iyalai, kwatankwacin bikin kirsimeti da ake gudanarwa a yammacin duniya.

A bana shekarar gargajiya ta Sin ta fara ne tun daga ranar Asabar din da ta gabata.

Wasu karin sassa na duniya da aka gudanar da shagulgulan bikin Bazara sun hada da Japan, inda 'yan kasar da dama suka nuna matukar sha'awa ga al'adun gargajiya na al'ummar Sinawa lokacin da ake tsaka da bukukuwan na sabuwar shekara. A Poland ma, an shakata da bukukuwan gargajiya a sassan kasar, ciki hadda biranen Warsaw da Wroclaw.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China