Sanarwar ta MOC ta kara da cewa, shagunan sayar da abinci da kayayyaki sun yi ciniki na kusan yuan biliyan 840 kwatan kwacin dalar Amurka biliyan 122.4, adadin da ya karu da kashi 11.4 cikin 100, idan aka kwatanta dana makamancin wannan lokaci a bara.
Cinikin kayayyakin da suka shafi bikin sabuwar shekara na gargajiya, da kayan ado, da na'urorin amfanin gida, da na'urorin zamani, sun samu matukar tagomashi a wannan lokaci na bukukuwan. Manyan kantunan sayar da kayayyakin ado a lardunan Gansu, Hebei da Anhui, rahotannin sun ce, sun ninka cinikinsu a wannan lokaci, hakan duk ya faru ne domin tasirin bukukuwan sabuwar shekarar zakara a bisa kalandar gargajiyar kasar Sin.
An bangaren sayar da abinci, baya ga yadda iyalai ke haduwa domin cin abinci tare, kantunan sayar da abinci suna aiki kafada da kafada da bangaren ciniki ta internet domin biyan muradun abokan huldarsu.