Kuma wannan adadin ya yi dai-dai da na shekarar da ta gabata, amma adadin fasinjojin da za su yi zirga-zirga ta jiragen kasa da na sama sun karu, yayin da a karon farko adadin masu tafiya da motoci ya ragu.
Ban da haka kuma, sakamakon karuwar layukan jiragen kasa masu saurin tafiya da aka gina a sassan fadin kasar Sin, an samu saukin tafiye-tafiye a wasu yankunan kasar Sin, musamman ma a yammacin kasar. (Maryam)