Hukumar ta bayyana cewa, tsakanin wadannan kwanaki, jiragen sama sama da 69,000 ne suka yi dakon fasinja, adadin da ya karu da kaso 12.9 bisa dari idan an kwatanta da makamancin lokaci a bara. Kaza lika adadin mutanen da jiragen suka dauka ya kai miliyan 9.84, adadin da shi ma ya karu da kaso 15.1 bisa dari sama da na bara.
Biranen da suka fi samun karuwar sufurin jiragen na sama dai sun hada Beijing, da Shanghai, da Guangzhou, da Shenzhen, da Kunming, da Chengdu da Chongqing, inda fasinjoji sama da 50,000 ke zirga zirga ta filayen jiragen su a kowace rana cikin makon na bikin bazara. (Saminu Hassan)