in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu gagarumar riba ta fannin yawon shakatawa a lokacin bikin bazara
2017-02-03 09:44:39 cri
Hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin(CNTA) ta bayyana cewa, ta samu ribar Yuan biliyan 423.3, kwatankwacin dala biliyan 61.7 a lokacin hutun bikin bazara na wannan shekara.

Hukumar ta ce hakan ba zai rasa nasaba da yadda karin mutane ke nuna sha'awar yin tafiye-tafiye a lokacin hutu ba.

Alkaluman da hukumar ta CNTA ta fitar sun nuna cewa, an samu karuwar kaso 15.9 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Rahotanni na cewa, a lokacin hutun na kwanaki bakwai wanda ya kare a jiya Alhamis, an yi tafiye-tafiye kimanin miliyan 444, adadin da ya karu da kaso 13.8 cikin 100 idan aka kwatanta da da na lokacin bara.

Hukumar ta ce Sinawa kimanin miliyan 6.15 ne suka yi bulaguro zuwa kasashen waje a lokacin wannan hutu,inda aka samu karuwar kaso 7 cikin 100 bisa na shekarar da ta gabata. Haka kuma miliyoyin Sinawa ne suka koma garuruwan su na asali domin ganawa da 'yan uwa da abokan arzikin a lokacin hutu.

A shekarar 2016, sashen yawon shakatawa na kasar Sin ya samu kudaden da suka kai Yuan Triliyan 3.9, kuma kasar ta Sin tana shirin kara kudaden shigar da ta ke samu daga wannan bangare zuwa Yuan Triliyan 7 nan da shekara ta 2020. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China