in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ba da lambobin yabo ga kungiyoyin yaki da jahilci na Afirka ta Kudu, Senegal da Indiya
2016-09-28 10:01:01 cri
A jiya Talata da dare ne, aka mika lambobin yabon ba da ilmi na Confucius na hukumar kyautata ilmi, kimiyya da al'ada ta MDD ta UNESCO a garin Confucius, watau birnin Qufu na lardin Shandong a kasar Sin. Kungiyoyin da suka karbi lambobin yabon sun hada da ma'aikatar da samar da ilmi a matakin farko ta kasar Afirka ta Kudu, sashen yaki da jahilci da bunkasa harsunan kalibun kasar Senegal, da kuma kungiyar samar da ilmi ga al'umma ta Malappuram mai zaman kanta da ke kasar Indiya.

A cikin jawabinta a yayin bikin ba da lambobin yabon, wakiliyar hukumar UNESCO dake kasar Sin Marielza Oliveria ta bayyana cewa, tun daga shekarar 2000, zuwa yanzu, an samu ci gaba sosai a harkokin yaki da jahilci a duniya. Amma duk da wannan nasara, ana fuskantar kalubaloli masu yawa. A halin yanzu, akwai baligai kimanin miliyan 781 da ba su iya karatu ko rubutu ba, kuma kimanin kashi 2 bisa 3 daga cikinsu mata ne, don haka, ya zama wajibi a daidaita wannan matsala.

Haka zalika, Marielza Oliveria ta ce, a halin yanzu, kasashen duniya sun fara aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, inda suka dukufa wajen cimma wannan buri cikin shekaru 15 masu zuwa, watau samar da ilmi ga al'ummominsu har tsawon rayuwarsu. Haka kuma, inganta harkokin yaki da jahilci ya kasance abu mai muhimminci a wannan jadawali. Muddin ana bukatar samun dauwamammen ci gaba a nan duniya, wajibi a tabbatar da cewa, ko wane mutum a duniya ya iya karatu da rubutu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China