Ministan wanda ya bayyana hakan Talatar nan yayin taron karawa juna sani kan harkokin ilimi na kasa, ya ce ma'aikatar ilimin za ta tsara yawan kudaden da gwamnatin za ta kashe kan makarantun renon kasar da kuma rangwamen da za a yiwa yaran dake karatu a makarantun reno masu zaman kansu.
Ya ce, za kuma a dauki managartan matakai game da biyan malamai albashi da abubuwan karfafa gwiwa a kan kari, da kuma kara takardun kwarewarsu na aiki.
Ministan ya ce gwamnati za ta karfafa tare da taimakawa makarantun reno masu zaman kansu da suka samar da hidima mai rangwame sannan suka kashe kudade wajen gina sabbin makarantun da fadada wadanda ake da su a yankunan karkarar kasar, da yankuna marasa ci gaba, da wurare da yankunan da ake da matukar bukatar makarantun sakamakon sassauta manufar kayyade iyali da gwamnati ta yi. (Ibrahim Yaya)