Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, ya jadadda ilimi a matsayin jigo da nahiyar Afrika za ta yi amfani da shi wajen yin takara da kasashen duniya.
Da yake jawabi ga taron shekara-shekara kan nahiyar Afrika a Dubai, Yoweri Museveni, ya ce dukkan kasashen nahiyar za su samar da wani dandali da zai zaburar da matasa, ta yadda za su raya nahiyar.
Ya ce, ilimi jigo ne, amma kuma akwai rikice-rikicen wariya da son kai.
Shugban ya yi kira ga daukacin al'ummar Afrika, su kawo karshen rikicin kabilanci su kuma yi tunanin samar da wani sabon karni a nahiyar, tare da habaka harkokin tattalin arziki, ta yadda nahiyar za ta iya takara da manyan kasashe kamar Amurka.
Da ya ke kira ga kasashen Afrika su ci gaba da cire shingayen cinikayya a cikin nahiyar, ya ce ya kamata nahiyar ta yi takara da Amurka, yana mai cewa, Uganda ba za ta iya ba ita kadai. (Fa'iza Mustapha)