Ya zuwa yanzu, an ba da lambobin kira kan fasahohi dubu 1356 a cikin gidan kasar Sin. Ban da haka kuma, adadin kudaden da kasashen ketare suka biya domin yin amfani da kayayyaki masu lambar kira na kasar Sin ya haura dallar Amurka biliyan 4.
Bugu da kari, kamfanoni guda 2788 sun cimma nasarar samun lambobin yabo a fannin ikon mallakar ilmi.
A halin yanzu kuma, ana koyar da ilmi mai alaka da hakan a makarantu kimanin 112, yayin da mutane sama da dubu dari 5 suka samu horaswa a wannan fanni a kasar ta Sin. (Maryam)