in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kafa dakunan karatu 587,000 a yankunan karkara
2017-12-19 10:21:35 cri

Wani taro kan dakunan karatu da aka yi jiya ya ce, kasar Sin ta kafa dakunan karatu 587,000 a yankunan karkara, inda suke taimakawa wajen inganta rayuwar al'ummar yankunan.

A cewar taron da aka yi a Shenyang, babban birnin lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar, an fara samar da dakunan karatun ne a shekarar 2005, inda suka fara aiki a shekarar 2007. Kuma tun bayan kammala kafuwar dakunan karatun a shekarar 2012 ne ake samar musu da litattafai tare da bude su ga al'umma.

Wata kididdiga ta bayyana cewa, a shekarar 2007 kowane mazauni yankin karkara ya mallaki matsakaici adadin littafi 0.13, ciki ban da litattafan karatu na dalibai. Adadin ya karu a bana, inda ya kai 1.63, kuma cikin shekaru 10 da suka gabata, an raba litattafai sama da biliyan 1.1 ga mazauna yankunan karkaar dake fadin kasar Sin.

Ba kadai inganta rayuwar al'ummar karkara dakunan suka yi ba, har ma da rage gibin dake tsakanin mazauna birnin da karkara tare da fitar da karin mutane daga talauci.

A cewar mataimakin shugaban hukumar yada labarai da wallafe-wallafe da kula da kafafen rediyo da talabijin da kuma fina-finai Zhou Huilin, har yanzu akwai matsaloli dake tattare da aikin dakunan karatun, inda ya ce akwai wasu dakunan karatun da har yanzu ba a cikakken amfani da su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China