in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta samar da karin makarantun koyar da sana'o'i
2017-10-10 11:24:59 cri
Hukumar kula da ilmin kasar Sin ta sanar da cewa, kasar za ta gina karin makarantun koyar da sana'o'i a yankunan karkara a matsayin wani bangare na yunkurin yaki da talauci.

Sun Yao, mataimakin ministan ilmin kasar Sin ya bayyana a lokacin taron koli kan yaki da talauci cewa, ilmin sana'a yana daya daga cikin ingantattun hanyoyi kuma hanya mafi sauri dake tsame al'umma daga cikin kangin talauci.

Sun, ya ce, sabbin makarantun za su samar da kyakkyawar kwarewa wanda ta dace da yanayin tattalin arzikin yankunan karkara da kuma yanayin da al'umma mazauna yankunan ke ciki.

Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin ta samar da tallafin kudade masu yawa ga dalibai masu fama da talauci don horas da su sana'o'i a duk fadin kasar, kana ta biyawa daliban kudaden makaranta da kuma samar musu guraben karo ilmi da kyautar kudade.

Ya zuwa karshen shekarar 2016, akwai Sinawa kimanin miliyan 43.35 wadanda kudin shigarsu na shekara ke kasa da yuan 2,300 kwatankwacin dalar Amurka 344, kusan kashi 3 bisa 100 na yawan al'ummar kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China