in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Antonio Guterres ya nuna damuwa kan batun Palasdinu da Isra'ila
2018-02-06 10:28:24 cri

Jiya Litinin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya nuna damuwarsa kan halin da ake ciki game da Palasdinu da Isra'ila, ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su ci gaba da daukar matakai na warware rikicin sassan biyu bisa shirin kafa kasashen Palasdinu da Isra'ila.

Mista Guterres ya yi jawabi a yayin taron kwamitin tabbatar da 'yancin al'ummar Palasdinu. Ya kara da cewa, yadda Isra'ila ta ci gaba da gina matsugunanta a yammacin gabar kogin Jordan, ya saba wa kudurorin MDD masu nasaba da hakan, da kuma dokokin kasa da kasa. Kazalika hakan ya haifar da babban cikas wajen wanzar da zaman lafiya. Ya ce aikace-aikace manu nasaba da nuna karfin tuwo, da kuma yadda ake rura wutar rikici, suna ci gaba da tsananta yanayin dar dar da kuma rashin amincewa da juna.

Mista Guterres ya ci gaba da cewa, halin da ake ciki a zirin Gaza ta fuskar jin kai da tattalin arziki yana dada lalacewa.

Kwanan baya, kasar Amurka ta rage yawan taimakon kudin da take bai wa ofishin kula da ayyuka da tallafawa Falasdinawa 'yan gudun hijira a yankin dake gabashin gabar bahar Mediterranean na MDD wato UNRWA. Dangane da lamarin, mista Guterres ya nuna damuwarsa sosai. Ya ce rashin isassun kudade zai raunana yadda ofishin yake bai wa Falasdinawa 'yan gudun hijira hidimomin ilmi da kiwon lafiya, lamarin da zai kawo illa ga Falasdinawa 'yan gudun hijira a yankin Gabas ta Tsakiya, da ma kwanciyar hankali a duk fadin yankin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China