in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya kama aiki
2018-01-31 13:57:23 cri

Jiya Talata bisa agogon birnin New York, Ma Zhaoxu, sabon zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya mikawa babban sakataren MDD Antonio Guterres, takardar shaidar cikakken wakilci a babban zauren MDD, inda ya nanata cewa, a ko da yaushe, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye martabar MDD da matsayinta.

A nasa bangaren, mista Guterres ya yi maraba da Ma Zhaoxu wanda ya fara aikinsa, ya kuma bayyana cewa, MDD tana son hada kai da Sin wajen kara tuntubar juna da hadin gwiwa, a kokarin raya hadin gwiwarsu zuwa sabon mataki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China