in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana damuwa game da yanayin tsaro a yankin yammacin Afirka da Sahel
2018-01-31 09:23:08 cri
Kwamitin sulhun MDD ya yi na'am da gagarumin ci gaban da aka samu a kasashen yammacin Afirka da dama,amma duk da wadannan nasarori, kwamitin ya bayyana damuwa matuka game da kalubalen tsaro dake addabar yankin.

Wata sanarwar shugaba da Kairat Umarov, shugabar kwamitin sulhun majalisar na watan Janairu ta gabatar, kwamitin mai mambobi 15 ya bayyana goyon bayansa ga wakilin musamman na MDD mai kula da yankin yammacin Afirka da Sahel Mohammed Ibn Chambas.

Haka kuma kwamitin sulhun ya yi maraba da yadda zabukan kasar Lebriya na shekarar 2017 suka gudana cikin lumana da yadda kasashen duniya suka mayar da hankali kan kasar, tun bayan janyewar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD(UNMIL) a ranar 30 ga watan Maris din shekarar 2017,inda suka jaddada muhimmancin rawar da hukumar tabbatar da zaman lafiya ta taka a wannan fanni.

Kwamitin sulhun ya kuma nanata damuwarsa game da halin da ake ciki a Guinea-Bissau, inda ya yi kira ga shugabannin siyasar kasar da su aiwatar da yarjejeniyar Conakry da aka cimma ba tare da wani bata lokaci ba. Sai dai kuma duk da yanayin da ake ciki a kasar Togo, kwamitin sulhun ya yaba da rawar da kungiyoyin yankin suka taka na lalubo bakin zaren warware matsalar ta hanyar tattaunawa.

A game da yanayin tsaro da ake ciki a yammacin Afirka da yankin sahel kuwa, kwamitin sulhun ya lura da yadda yawaitar hare-haren ta'addanci da fashin teku da wasu munannan ayyuka ke haifar da barazana, ciki har da safarar bil-Adama da miyagun kwayoyi da albarkatun kasa da sauransu.

Yankin Sahel dai yana tsakanin Afirka ne da yankin Sahara ta arewa kana ya yi iyaka da yankin Sunadian Savanna daga kudu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China