in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da AU za su inganta hadin-gwiwa wajen raya Afirka
2018-01-28 13:20:05 cri
Jiya Asabar da safe, babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka AU, Moussa Faki Mahamat, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kulla abokantaka a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda suka yi alkawarin karfafa hadin-gwiwa a fannonin da suka shafi raya harkokin Afirka gami da sauran wasu batutuwan duniya.

Antonio Guterres, ya bayyana a wajen taron manema labarai cewa, alakar abokantaka tsakanin MDD da AU na da matukar muhimmanci, kuma inganta hadin-gwiwa tare da AU wani muhimmin aiki ne wanda ya kamata MDD ta dauki nauyin gudanarwa. Zaman lafiya, da tsaro, da cigaba, gami da hakkin dan Adam su ne muhimman fannonin da bangarorin biyu za su inganta hadin-gwiwa tsakaninsu.

Guterres ya kara da cewa, Afirka na da kwarewa wajen lalibo bakin zaren daidaita matsalolin duniya. Idan kasashen Afirka basu iya baiwa matasansu kwarin-gwiwar su yi aiki tukuru ba, kasashen duniya ba zasu samu ci gaba ba. Haka kuma, idan kasashen Afirka basu iya yin rigakafi gami da daidaita matsalar tashe-tashen hankali ba, kasashen duniya ba zasu iya cimma burin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.

Har wa yau, Guterres ya nanata cewa, MDD na goyon-bayan shugabannin kasashen Afirka wajen daidaita matsalolin kasashensu bisa ikon kansu, kana zata dukufa wajen samar da taimako ga Afirka gami da kungiyar ta AU.

A nasa bangaren, Moussa Faki Mahamat, ya jaddada cewa, kungiyar tarayyar Afirka na maida hankali sosai kan raya huldar abokantaka da MDD, inda ya godewa Antonio Guterres saboda matukar kokarin da ya yi na fadada hadin-gwiwa tsakanin AU da MDD. Faki ya kuma ce, MDD da AU suna ta kokarin daidaita manyan tsare-tsare gami da manufofinsu domin tinkarar sabbin kalubaloli.

Antonio Guterres ya isa birnin Addis Ababa na kasar Habasha ne a ranar 26 ga wata, don halartar taron kolin kungiyar tarayyar Afirka karo na 30 daga ranar 28 zuwa 29 ga watan nan.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China