in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da AU za su kara hadin gwiwa a fannonin kiyaye zaman lafiya da tsaro
2018-01-29 10:20:19 cri
Babban sakataren MDD António Guterres ya bayyana yayin da yake halartar taron kolin kungiyar AU karo na 30 a birnin Addis Ababa dake kasar Habasha cewa, MDD da kungiyar AU za su kara hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin kiyaye zaman lafiya da tsaro, samun bunkasuwa mai dorewa, kare 'yancin mata da matasa da yara, batun bakin haure, yaki da cin hanci da rashawa da sauransu don inganta dangantakar hadin gwiwar dake tsakanin MDD da kungiyar AU.

Game da batun kiyaye zaman lafiya da tsaro, Guterres ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin MDD da AU tana da muhimmanci sosai wajen samar da duniya mai cikakken tsaro.

Sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD su kadai ba za su iya warware dukkan matsaloli ba, akwai bukatar sojojin kiyaye zaman lafiya da yaki da ta'addanci daga bangarori daban daban da su shiga aikin kiyaye zaman lafiya na duniya.

Game da samun bunkasuwa mai dorewa kuwa, a yayin taron kolin kungiyar AU na wannan karo, MDD da AU sun daddale ajandar aiwatar da ayyukan samar da ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2063 da tsarin ajandar shekarar 2030. Guterres ya yi nuni da cewa, yin hadin gwiwa tare da kungiyar AU shi ne zabi mafi dacewa ga MDD bisa manufa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China