A ganawarsa da manema labarai bayan ya gabatar da takardarsa ta kama aiki a matsayin wakilin kasar Sin a MDD ga babban magatakardan MDD, Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ba da gudummawa na kashin kanta a kokarin da ake na kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa ta hanyar girmama juna, nuna adalci da cin moriyar juna, da gina al'umma mai kyakkyawar makoma.
Ya kara da cewa, a matsayinta na zaunanniyar mamba a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin za ta dukufa wajen kare matsayi da kuma martabar MDD yadda ya kamata, za kuma ta goyi bayan rawar da MDD take takawa. Haka kuma, ya ce, kasar Sin za ta sauke nauyin dake kanta na kasa na kasa sannan za ta shiga a dama da ita a kokarin da ake na tafiyar da harkokin kasa da kasa gyaran fuska. Haka kuma zai ci gaba da baiwa manufofi da shirye-shiryen kasar Sin goyon baya, kuma kasar Sin za ta ci gaba da zama mai kokarin tabbatar da lafiya da ci gaban duniya da kuma kiyaye dokokin kasa da kasa. (Maryam)