A wajen taron, Mr. Ma Zhaoxu, ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru sama da 70 da kafa MDDr, mambobinta sun karu daga 51 zuwa 193, kuma akasarinsu kasashe masu tasowa ne, a yayin da kasashen Afirka suka zarce rubu'i na baki dayan mambobin. A halin da ake ciki yanzu, kasashe masu tasowa da ma kasashen Afirka suna kara tasirinsu, don haka, ya kamata a kara musu wakilci a yayin da ake yiwa MDD kwaskwarima, ta yadda zasu iya kara bayyana ra'ayoyinsu a yayin da kwamitin sulhu ke tsaida duk wani kuduri.
Mr. Ma Zhaoxu ya ce, kullum kasar Sin na goyon bayan yiwa kwamitin sulhu gyare-gyaren da suka dace, kuma tana son hada kan sassa daban daban na duniya, don gudanar da wannan aiki bisa ga moriyar bai daya ta illahirin mambobinta da kuma samar da kyakkyawar makoma ga MDDr.(Lubabatu)