in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in tattalin arzikin Falesdinu ya bukaci a daina yin amfani da kudin Isra'ila
2018-02-06 10:24:00 cri
A Jiya Litinin ne shugaban kwamitin tattalin arziki na hukumar neman bunkasuwa da sake ginawar kasa ta Falesdinu Mohamed Ishteyah ya bayyana cewa, ya kamata a dakatar da yin amfani da kudin Isra'ila a fadin Falesdinu, domin aiwatar da kudurin kungiyar 'yantar da al'ummar Falesdinu da abin ya shafa, ta yadda za a kawar da dogaron da Falesdinu ke yi da Isra'ila ta fuskar tattalin arziki.

Haka kuma, ya ce, karancin kudaden Falesdinu ya haddasa raguwar tattalin arzikinta, yayin da ake karfafa dogaro kan Isara'ila. Ya ce, ya kamata a yi amfani da sauran kudade da ake iya samu ta wasu sassa a yankunan Falesdinu amma ban da na Isra'ila.

Sa'an nan, ya jaddada cewa, ya kamata a dauki matakai da dama domin cimma wannan buri, musamman ma a fannin karfafa kwarewar al'ummomin kasar wajen samar da kayayyaki ta fuskar ayyukan noma, da masana'antu. A sa'i daya kuma, a dakatar da shigar da hajojin Isra'ila a yankunan Falasdinawa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China