in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ismail Haniyeh ya lashe zaben shugaban hukumar siyasar kungiyar Hamas
2017-05-07 12:57:30 cri
Kakakin reshen kungiyar Hamas dake zirin Gaza ya fidda wata sanarwa a jiya Asabar, inda ya gaskata cewa, Ismail Haniyeh ya lashe babban zaben shugaban hukumar siyasa ta kungiyar.

Cikin sanarwar, an kuma bayyana cewa, duk da cewa an gamu da matsaloli da dama, amma kungiyar ta cimma nasarar gudanar da zaben cikin yanayin zaman lafiya yadda ya kamata. Kana, shugabannin kungiyar Hamas sun halarci taron wadanda suke da zama a birnin Doha na kasar Qatar da yankin Gaza ta tsarin bidiyo daga nesa, inda suka nuna goyon baya ga Ismail Haniyeh da ya maye gurbin sabon shugaban hukumar siyasa na kungiyar.

Amma, cikin sanarwar, ba a yi bayani kan ko Ismail Haniyeh zai gudanar da aikinsa a yankin Gaza ko a birnin Doha ba, wanda a halin yanzu yake kasancewa a yankin Gaza.

A shekarar 1987, aka kafa kungiyar Hamas, wadda take sa ran rushe Isra'ila ta hanyar yake-yake, shi ya sa, Isra'ila da kunigyar tarayyar kasashen Turai da kuma kasar Amurka suka mayar da kungiyar Hamas a matsayin kungiyar 'yan ta'adda. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China