Rahotanni sun bayyana cewa, yayin ganawar tasu a jiya Jumma'a, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya jaddada cewa, ba za a sauya yanayin da Masallacin ke ciki ba, har sai bangarorin da ke adawa da juna sun dauki matakan da za su dace na tsayar da rikice-rikicen dake tsakaninsu.
Da safiyar jiya Juma'a ne, wasu mutane uku suka budewa 'yan sandan Isra'ila wuta a tsohon birnin Jerusalem, harin da ya haddasa mutuwar 'yan sanda biyu, daga bisani kuma, 'yan sanda sun harbe maharan 3.
Bayan aukuwar harin ne kuma, Isra'ila ta rufe Masallacin Al-Aqsa dake wurin, al'amarin da ya hana Musulmai yin salla a masallacin. Baya ga wannan, Isra'ila ta kuma kulle kofar fita ta birnin dake yammacin kogin Jordan. (Maryam)