Li wanda ya bayyana hakan Litinin din nan,yayin bikin shekara-shekara da ya gudana a nan birnin Beijing na karrama masana da masu binciken kimiyya da fasaha da suka taka rawar gani, ya kara da cewa, akwai bukatar a kara zage damtse wajen kare ingancin abinci da magance gurbatar iska ta yadda jama'a za su samu rayuwa mai inganci.
Bugu da kari, firaministan na Sin ya kara yin kira da a hade kimiyya da fasahar kirkire-kirkire wajen gudanar da tattalin arziki sannan a inganta ci gaban sabbin fasahohi, sabbin masana'antu da sabbin kasuwanci.(Ibrahim)