Wannan ce ziyara ta farko da firaministan kasar Sin ya kai wata kasa ta waje a shekarar 2018. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Kong Xuanyou ya bayyanawa 'yan jarida a kwanakin baya cewa, wannan ce ziyara ta farko da kasar Sin ta shirya gudanarwa a fannin diplomasiyya, wadda ke da babbar ma'ana ga hadin gwiwar yankunan kogin Lancang da kogin Meigong, kana za ta haifar da babban tasiri ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Cambodia a nan gaba. (Zainab)