in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang: Kasashen LMC sun amince su zurfafa hadin gwiwa da juna
2018-01-11 09:35:26 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce kasashen dake kewayen kogunan Lancang da Mekong da suka hada da Sin da Cambodia, da Myanmar, da Laos, da Thailand da Vietnam, sun amince su zurfafa hadin gwiwa tsakanin su.

Mr. Li wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin taron jagororin kungiyar kasashen 6 da ake wa lakabi da LMC, ya ce kasashen na fatan zurfafa hadin kai mai cike da adalci, za kuma su yi aiki tukuru kafada da kafada domin cimma nasarar hakan.

A taron LMCn na bana, kasashen 6 sun kuma amince da wasu kundin bayanai guda biyu, wato na shirin aiwatar da manufofin su tsakanin shekarun 2018 zuwa 2022, da kuma yarjejeniyar Phnom Penh.

Sau da yawa dai a kan samu rashin jituwa tsakanin kasashen dake kewayen koguna kamar na Lancang da Mekong, wanda hakan a cewar Mr. Li, ya sa kasar Sin ke fatan warware duk wata takaddama mai alaka da hakan cikin ruwan sanyi, kuma ta yadda dukkanin sassa za su amfana.

Ya ce, Sin na fatan wanzar da zaman lafiya tsakanin ta da makwaftan ta, da bunkasa ci gaba a zamanance, da yaki da fatara, don haka ta gabatar da shawarar kafa tsarin kungiyar LMC da zai amfani dukkanin sassan 6.

Daga nan sai ya jaddada matsayin kasar Sin na ci gaba da goyon bayan kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta ASEAN, wadda ke da burin ganin dukkanin sassan yankin sun ci gajiya tare, baya ga wadda za su samu daga hadin gwiwar kungiyar ta LMC.

Li Keqiang ya ce, a taron na bana, kimanin ayyuka 200 aka riga aka mika domin tantancewa. Kuma ana fatan dukkanin kasashen da ke da ruwa da tsaki a ayyukan, za su shiga a dama da su domin cimma nasarar da aka sanya gaba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China