A yau Laraba ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa birnin Phnom Penh na kasar Combodia,bisa gayyatar da takwaransa na kasar Samdech Hun Sen ya yi masa, don halartar taron koli karo na 2 na hadin kan yankunan kogin Lancang da Mekong, wato LMC a takaice, tare kuma da kai ziyara kasar.
LMC wani sabon tsarin hadin gwiwa ne da kasashen Sin, Myanmar, Laos, Thailand, Combodia da kuma Vietnam suka kafa. (Bilkisu)