in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a kara zuba jari kan ayyukan raya yankunan karkarar Sin
2018-02-05 13:39:34 cri

Shugaban ofishin ba da jagoranci kan ayyukan yankunan karkara na kwamitin tsakiyar kasa ta Sin Han Jun ya bayyana a yau Litinin cewa, manufar farfado da yankunan karkara ta kasar Sin, babbar manufa ce ta Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da gwamnatin kasar Sin, kuma aiki ne mai muhimmanci dake daukar dogon lokaci.

Mr. Han ya jaddada cewa, idan ana son farfado da yankunan karkara na kasar, ya kamata a zuba jari kan aikin, yayin da ake tsara manufofin da za su dace da ciyar da ayyuka masu alaka da hakan gaba.

A yau Litinin, ofishin labarai na gwamnatin kasar Sin ya kira taron manema labarai, inda aka yi bayani kan wata sabuwar takarda da gwamnatin kasar ta fidda mai taken "Ra'ayoyin gwamnatin kasar Sin kan aiwatar da manufofin farfado da yankunan karkara na kasar Sin", inda aka yi bayani kan yadda za a inganta ayyukan gona na zamani a yankunan karkara, da kuma farfado da yankunan karkara na kasar Sin bisa tsarin gurguzu na kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China