An fara daukar wannan mataki ne a bara, inda aka yi kokarin gina wasu wurare na musamman da jama'a za su iya karanta littafi a cikinsu, sa'an nan aka sanya jama'a su shiga a dama da su, don yayata dabi'ar karantawa a wadannan wurare na musamman da aka tanada.
Ban da haka, an ba jama'a damar zabar wasu littattafan da suke so a madadin laburare wanda ke da bukatar sayen karin littattafai. Bisa wannan shiri, jama'a za su iya samun littattafai a kantunan sayar da littattafai a kyauta domin su karanta a gida, daga bisani za su iya mayar da littattafan ga dakunan karatu domin ajiye su. Ta wannan mataki, jama'a za su samu damar karanta karin littattafai, yayin da dakunan karatu suka samu littattafan da ake son karantawa. (Bello Wang)