in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afrika zasu zurfafa mu'amala a tsakanin al'ummominsu
2018-02-03 14:03:24 cri
Jami'an kasashen Afrika da na Sin sun nanata aniyarsu cewa bangarorin biyu zasu zurfafa mu'amala ta hanyar karfafa dangantaka tsakanin al'ummominsu da fahimtar juna wajen cimma ajandar samar da cigaba da kyakkyawar makoma.

Kungiyar raya cigaban harkokin diplomasiyya ta kasar Sin, da ofishin jakadancin kasar Sin a kasar Habasha, da ofishin wakilci na kasar Sin a kungiyar tarayyar Afrika (AU), a ranar Juma'a sun shirya wani taron karawa juna sani na hadin gwiwa mai taken, Sin da Afrika: Mu'amala tsakanin mutum da mutum don kyakkyawar fahimtar juna, wanda aka gudanar a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

A jawabinsa na bude taron, Tan Jian, jakadan kasar Sin a Habasha, ya bayyana sha'awar da kasar Sin keda ita game da kara zurfafa dangantaka da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika karkashin lemar shawarar ziri daya da hanya daya.

Jakadan ya nanata cewa, kasar Sin tana cigaba da fadada shawarar ziri daya da hanya dayatare da samun tsayayyen goyon bayan kasar Habasha da sauran kasashen Afrika.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar zumunta ta mutanen Sin da Habasha (ECPFA), Hailekiros Gessesse, ya yaba da irin gudumowar da kasar Sin ke bayarwa wajen cigaban nahiyar Afrika ta hanyar zuba jari a fannoni masu yawa.

Da yake nuna yabo game da hadin gwiwar Sin da Afrika, mataimakin shugaban kungiyar tarayyar Afrika AU, Kwesi Quartey, ya bayyana cewa, kungiyar ta Afrika tana cigaba da yin kokarin shawo kan tsalalolin talauci a Afrika da kuma kara dunkulewar nahiyar ta hanyar tsare tsare kamar kafa tsarin ciniki cikin 'yanci a nahiyar, inda kungiyar ta AU ke yin aiki tare da kasar Sin wajen cimma wannan buri.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China