in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mazauna birane na Sin ya karu zuwa kashi 58.52 bisa dari
2018-02-05 13:38:41 cri
Bisa bayanin da hukumar kididdiga ta yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2017, yawan mazauna birane na kasar Sin ya kai miliyan 813.47, adadin da ya karu da mutum miliyan 20.49 idan aka kwatanta da na shekarar 2016. Lamarin da ya sa, adadin mazauna birane na kasar Sin ya kai kashi 58.52 bisa dari, wanda ya karu da kashi 1.71 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2016.

Shugaban hukumar Mao Youfeng ya ce, karuwar adadin za ta habaka bukatun al'ummomin kasar Sin, da kuma kyautata ingancin ayyukan samar da kayayyaki, ta yadda za a kyautata ayyukan ba da hidima ga al'ummomin kasar.

Haka kuma, ana ganin cewa, adadin mazauna birane na kasar Sin bai kai matsayi na kasashe masu arziki, wadanda matsayin su ya kai kimanin kashi 80 bisa dari. Lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin za ta ci gaba da neman bukasuwa kan wannan aiki, wanda zai ba da taimako wajen ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin ta gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China