in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da aikin gina lambun shan iska na dankon zumunci tsakanin Sin da Afirka a Habasha
2018-02-03 14:09:27 cri
Jiya Jumma'a a hedikwatar kungiyar tarayyar Afirka wato AU a birnin Addis Ababar kasar Habasha, aka yi bikin kaddamar da aikin gina lambun shan iska mai sada zumunta tsakanin Sin da Afirka, wanda kasar Sin ta bada taimakon ginawa. Mataimakin shugaban hukumar kungiyar AU, Thomas Kwesi Quartey, da shugaban tawagar kasar Sin dake AU, Kuang Weilin sun halarci bikin.

Kuang ya ce, lambun shan iska da za'a gina, alama ce ta dankon zumunci tsakanin Sin da Afirka. Kasar Sin zata ci gaba da goyon bayan hada shawarar 'ziri daya da hanya daya' da ajandar AU ta raya Afirka nan da shekara ta 2063, da nuna sahihanci da kara zumunta da hadin-gwiwa da kasashen Afirka, a wani kokari na samar da taimako ga AU gami da duk nahiyar ta Afirka.

A nasa bangaren, Thomas Kwesi Quartey, ya nuna yabo ga taimako da tallafin da kasar Sin ta baiwa AU. Quartey ya ce, akwai dadadden zumunci tsakanin Afirka da Sin. A shekarun 1970, duk da matsalolin da kasar Sin ke fuskanta, ta taimakawa Afirka shimfida layin dogo tsakanin Tanzaniya da Zambiya. Yanzu gwamnatin Sin ta bullo da shawarar 'ziri daya da hanya daya', abun da ya samar da sabbin damammaki wajen inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka da raya nahiyar Afirka baki daya.

Wannan lambun shan iska mai nuna zumunci tsakanin Sin da Afirka, wato China-Africa Friendship Garden a Addis Ababar Habasha, fadinsa ya kai murabba'in mita dubu biyu, wanda cibiyar nazarin tsara fasalin gine-gine ta jami'ar Tongji ta kasar Sin ta tsara fasalinsa. Lambun ya kasu gida biyu, wato bangare na nuna al'adun Afirka da kuma bangare na al'adun kasar Sin, wanda ke nuna kyakkyawar alaka da hadin-gwiwa gami da dankon zumunci tsakanin Sin da Afirka.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China